ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’id Khadib Zade yana fadar cewa, ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif zai halarci taron kan kasar Afghanistan ta kafar sadarwa ta Bidiyo. Kasashen Afganistan Findland da kuma MDD ne suka saba shirya taron bayan shekaru hudu-Hudu.
A taron na kwanaki biyu wanda wakilan kasashe 66 zasu halatta da kuma kungiyoyin kasa da kasa 32, an saba tattauna matsalolin kasar ta Afgansitan wadanda suka hada da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar da kuma batun sake tada komatsar tattalin arzikin kasar.
A dai-dai lokacinda aka fara wannan taron a birnin Geneva, an bude wani taron sulhuntawa tsakanin gwamnatin kasar ta Afgansitan da kuma kungiyar Taliban a birnin Doha na kasar Qatar.
342/